Akalla ’yan Nijeriya 42 ne aka kora daga yankin Ashanti na ƙasar Ghana bayan hukuncin kotuna kan laifuffuka da suka haɗa da karuwanci, zamba da wasu laifuka makamantansu.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ministan yankin Ashanti, Frank Amoakohene, ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce an kuma kori ’yan Kamaru 13, ’yan Ivory Coast 3, ’yan Burkina Faso 3 da ’yan Benin 7, wanda ya kai adadin mutanen da abin ya shafa 68 baki ɗaya.
Ministan ya yaba wa Hukumar Shige da Ficen Ghana bisa yadda ta aiwatar da dokoki tare da mutunta haƙƙin ɗan Adam.
Matakin ya zo ne yayin da ake ƙara samun rahotannin tsananta sa ido da kama ’yan Nijeriya a ƙasashen waje kamar yadda rahoton jaridar Punch ta ruwaito.
