Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiMajalisar Dokokin Taraba ta musanta cewa Kakakinta ya raba Naira 1000 a...

Majalisar Dokokin Taraba ta musanta cewa Kakakinta ya raba Naira 1000 a matsayin barka da Kirsimeti

Majalisar Dokokin Jihar Taraba tare da Zing Watch Group sun musanta rahotannin da ke yawo cewa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba, John Bonzena, ya raba Naira dubu dai-daya ga al’ummar mazabarsa a matsayin barka da Kirsimeti.

Musantawar ta biyo bayan rahotannin da suka ce wasu mata da matasa daga yankin karamar hukumar Zing sun nuna rashin jin daɗi bayan an ce an gayyaci kusan mutum 37 zuwa gidan Kakakin Majalisar a Jalingo domin karɓar kyautar barka da Kirsimeti.

Rahotannin sun yi ikirarin cewa mutanen, da aka zaɓo daga mazabu daban-daban a Zing, sun je Jalingo ne da fatan samun tallafi mai yawa, amma daga bisani suka zargi cewa Kakakin Majalisar ya ba su N1,000 kacal, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce.

Sai dai a cikin sanarwarsu ta manema labarai daban-daban da aka fitar a ranar Asabar, Majalisar Dokokin Jihar Taraba da Zing Watch Group sun bayyana cewa kyautar ba ta shafi baƙin da suka zo daga Zing ba. Sun ce an tanadi tallafin ne ga yara da matan da ke zaune a unguwar da Kakakin Majalisar ke zaune a Jalingo, ba don baƙin mazabarsa ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata