Tsohon Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanatan Kogi ta Tsakiya a zaben shekarar 2027.
Yahaya Bello ya sanar da hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai fadar Basarake Ohinoyin Ebiraland, inda ya gana da sarakunan gargajiya, shugabannin addini da jagororin al’umma daga yankin.
Jaridar Punch ta rawaito cewa an wallafa bidiyon ziyarar da kuma sanarwar tsayawa takarar a shafinsa na Facebook a ranar Litinin.
