Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiSabbin dokokin haraji za su fara aiki a 1 ga Janairu 2026...

Sabbin dokokin haraji za su fara aiki a 1 ga Janairu 2026 — Tinubu

Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da cewa sabbin dokokin haraji za su fara aiki a ranar 1 ga Janairu, 2026, kamar yadda aka tsara tun da farko. Dokokin, ciki har da waɗanda suka fara aiki a ranar 26 ga Yuni, 2025, an bayyana su a matsayin wata dama ta musamman wadda ake samu sau ɗaya a ƙarni domin gina tsarin kuɗaɗen ƙasa.

A cikin wata sanarwa da Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya sanya wa hannu, ya jaddada cewa dokokin ba wai an ƙirƙire su ne domin ƙara haraji ba, illa dai domin gyara tsarin haraji gaba ɗaya, daidaita dokoki, da kare mutuncin ‘yan ƙasa tare da ƙarfafa alaƙar amincewa tsakanin gwamnati da jama’a. Ya kuma buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki su goyi bayan matakin aiwatarwa da aka shiga yanzu.

Shugaban ƙasar ya ce duk da hayaniyar da ake yi kan zargin sauye-sauye a wasu sassan dokokin, babu wata babbar matsala da aka tabbatar wadda za ta hana ci gaba da gyaran. Ya tabbatar da cikakken bin doka da oda, tare da alkawarin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da Majalisar Dokoki domin warware duk wata matsala da ka iya tasowa, yana mai tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnati za ta ci gaba da aiki bisa muradin jama’a domin samar da tsarin haraji da ke tallafa wa cigaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata