Sunday, April 5, 2026
HomeLabarai'Yan bindiga sun sace wani basarake da dansa a jihar Kwara

‘Yan bindiga sun sace wani basarake da dansa a jihar Kwara

Fargaba ta mamaye zukatan al’ummar Aafin da ke yankin Ile Ere a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara, bayan da ’yan bindiga suka sace Sarkin Aafin, Oba Simeon Olaonipekun, tare da guda daga cikin ’ya’yansa mai suna Olaolu.

 

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa an sace sarkin ne a daren Laraba yayin da wasu ’yan bindiga kusan takwas suka kai hari fadarsa, inda suka rika harbi ta ko ina kafin su kutsa kai ciki.

 

Wani ɗan uwa daga cikin iyalan sarkin da ke fadar a lokacin harin ya ce maharan sun zo ne kai tsaye domin daukar sarkin da matarsa, ganin hakan yasa suka rufe kofofin gidan amma da ‘yan bindigar suka fuskanci haka suka rika harbi ta ko ina.

 

Har zuwa wannan lokaci dai babu wata sanarwa daga mahukunta kan lamarin, sai dai al’ummar sun bukaci daukar mataki cikin gaggawa don ceto wadanda aka sace.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata