Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiSojoji sun dakile harin ‘yan bindiga a wasu kauyukan Kano

Sojoji sun dakile harin ‘yan bindiga a wasu kauyukan Kano

Rundunar sojin Nieriya ta ce ta dakile yunkurin harin ‘yan bindiga da suka yi kokarin shiga wasu al’ummomi a Shanono na Jihar Kano, bayan gumurzu mai tsanani da ya dauki tsawon lokaci.

Artabun ya fara ne a daren Alhamis zuwa wayewar Juma’a, inda aka gwabza fada a kauyukan Yankwada, Babanduhu da wasu makwabtansu a yankin.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga News Agency of Nigeria, kakakin rundunar sojin Nijeriya a Kano, Zubair Babatunde, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi kokarin kutsawa kauyukan ne ta kan babura, suna harbe-harbe ba kakkautawa.

Babban jami’in ya kara da cewa harin ramuwar gayya ne, biyo bayan asarar da ‘yan bindigar suka yi a makon da ya gabata, lokacin da sojoji suka yi musu mummunan luguden wuta a wani artabu da suka yi da su.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata