Kungiyar Likitocin masu neman kwarewa NARD ta bayyana cewa za ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga Litinin, 12 ga Janairu, 2026, sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen cika yarjejeniyar da aka cimma da su.
Shugaban kungiyar, Dakta Mohammad Suleiman, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafinta na X a karshen makonnan, bayan taron gaggawa da aka gudanar a ranar Jumma’a.
Ya ce yajin aikin, zai fara ne idan har gwamnatin tarayya da ma’aikatar Lafiya ba su aiwatar da yarjejeniyar da aka rattaba hannu da ƙungiyar ba.
