Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da tuhumar laifi da Gwamnatin Nijeriya ta shigar kan Sanata mai wakiltar Kogi Ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, lamarin da ya kawo karshen shari’ar da ta tayar da kura a fadin Nijeriya.
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan Ofishin Babban Lauyan Nijeriya ya shigar da sanarwar janye kara, lamarin da ya sa alkalin kotun, Mai shari’a C. N. Oji, ya goge tuhumar bata suna da sauran laifukan da aka dora wa Sanatar, wadda ta samo asali daga kalaman da ta yi a wata hira ta talabijin.
Mai shari’a Oji ya ce matakin ya nuna bukatar takatsantsan wajen amfani da ikon shigar da kara, yana mai fatan hakan zai karfafa mutunta doka da tsarin dimokuradiyya. Lauyan gwamnati ya tabbatar wa kotu cewa an janye karar ne domin amfanin adalci da amincewar jama’a ga tsarin shari’a.
Da take martani bayan zaman kotu, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce hukuncin ya tabbatar da imaninta ga doka, tana mai jaddada kudirinta na ci-gaba da yi wa al’ummarta hidima da kare ’yancin dimokuradiyya, tare da gode wa lauyoyinta da magoya bayanta.
