Rundunar ‘yan sandan Jihar Edo ta kama wani mai sana’ar faci mai shekaru 34 mai suna Idris Isiaka, bisa zargin kirkirar sace kansa domin karbar kudin fansa daga iyalansa. Lamarin ya faru ne a Emaudo, Ekpoma da ke Karamar Hukumar Esan West.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Eno Ikoedem, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 10 ga Janairu, inda Isiaka tare da wasu abokan aikinsa biyu da ke gudun hijira suka yada labarin sace shi a kafafen sada zumunta tare da neman kudin fansa Naira miliyan 12.
Ya ce bayan kirkirar satar, nan take suka shirya yada labarin ta hannun wani blogger, sannan suka tuntubi iyalan wanda ake zargin da ke Jihar Kogi, suna barazanar kashe shi idan ba a biya kudin fansar ba.
Ikoedem ya ce dan’uwan wanda ake zargin ya sayar da kadarorinsa tare da biyan wani bangare na kudin fansar, wanda daga bisani Isiaka ya raba da abokan aikinsa. Ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa, kuma za a gurfanar da shi gaban kotu bayan kammala bincike.
