Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiYadda muke shiga haɗari wajen tsallakawa Jamhuriyar Nijar saboda barazanar Turji —...

Yadda muke shiga haɗari wajen tsallakawa Jamhuriyar Nijar saboda barazanar Turji — Mazauna Sokoto

Wasu ‘yan gudun hijira daga Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sokoto sun koka kan ƙaruwa hare-haren ‘yan bindiga a yankin, inda suka ce ‘yan uwansu na shiga mummunan haɗari wajen tsallakawa zuwa Jamhuriyar Nijar domin tsira da rayukansu.

Sun shaida wa Saturday PUNCH cewa ‘yan uwansu sun tsere zuwa ƙasar makwabciya ne bayan sabbin barazana da hare-hare daga ‘yan bindigar da ke biyayya ga shahararren shugaban ‘yan ta’adda, Bello Turji. Wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta a makon nan ya nuna jama’a na guduwa daga wasu ƙauyuka, lamarin da hukumomi suka tabbatar.

Sakataren Kungiyar Raya Yankin Gabashin Sokoto, Farfesa Mu’azu Shamaki, ya ce fara wannan kaura ya biyo bayan barazanar da Turji ya yi wa wasu ƙauyuka da ke kewaye da Tidibali, wani gari a cikin ƙaramar hukumar.

Ya ce tun daga ranar Juma’ar da ta gabata, jama’a da dama ke tururuwa zuwa hedikwatar ƙaramar hukumar domin kai ƙorafi, inda ya ƙara da cewa fiye da kauyuka 20 suka riga suka yi hijira saboda tsoron hare-haren.

A hirarraki daban-daban, tsoffin mazauna yankin sun ce iyalai da ‘yan uwansu na tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar. Wani daga cikinsu, Mohammed Saleh, wanda ke Dole Kaina — wani yankin kan iyaka tsakanin Nijeriya da Nijar a Sabon Birni — ya ce mutane da dama na ɗaukar haɗarin tsallaka iyaka domin neman mafaka da tsaro.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata