Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiJihar Kebbi ta ayyana 11 da 14 ga Fabrairu a matsayin ranakun...

Jihar Kebbi ta ayyana 11 da 14 ga Fabrairu a matsayin ranakun bikin Kamun Kifi na Argungu na duniya

Gwamnatin Jihar Kebbi ta sanar da cewa za a gudanar da Bikin Kamun Kifi na Duniya na Argungu daga 11 zuwa 14 ga Fabrairu na wannan shekara.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Martaba Sarkin Argungu, Alhaji Samaila Mera ya bayyana wa ’yan jarida, bayan wani taro da aka yi da Kwamitin Tsare-tsaren Bikin na Jiha da Kwamitin Shirya Biki na Masarautar Argungu, a Ofishin Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi ranar Juma’a, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Sarkin Argungu ya bayyana cewa bikin kamun kifin ya samo asali ne a matsayin matakin samar da zaman lafiya tsakanin ’yan jihadin Daular Usmaniyya ta Sakkwato da Masarautar Kanta, kafin daga bisani ya zama wani babban bikin al’adu.

Ya ƙara da cewa, saboda muhimmancin tarihin bikin, UNESCO ta amince da shi a matsayin bikin al’adu na kasa da kasa, sannan bayan Yaƙin Basasar Nijeriya, an yi amfani da bikin wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa da zaman lafiya.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata