Shugaban jam’iyyar APC na Nijeriya Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa ba za su bai wa duk wanda ba dan jam’iyya mukami ba bayan zaben 2027.
Farfesa Nentawe ya fadi haka ne a Abuja, inda ya jaddada cewa wajibi ne kowane mai mukami ya zama mai biyayya ko kuma aiki da jam’iyyar da ta ba shi matsayin.
A cewar sa, babu maganar bai wa kwararru ko wasu masana mukamai a jam’iyyar, yana mai dogaro da cewa a bisa tsarin siyasa ake tafiya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
