Wasu ‘yan majalisar tarayyar Nijeriya masu ci da kuma tsoffi da suka hada da mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau I. Jibrin, tsohon kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, da tsohon shugaban majalisar dattawa Anyim Pius Anyim, sun bukaci a saka tsarin karba-karbar mulki tsakanin yankin Arewa da Kudu cikin kundin tsarin mulki domin tabbatar da adalci da daidaito a rabon mulki.
Wannan kira ya zo ne yayin da majalisar tarayya ke shirin kada kuri’a kan kudirin gyaran kundin tsarin mulki bayan dawowar ta daga hutun da ta dauka.
Sun bayyana matsayinsu ne a ranar Asabar yayin taron koli na tsofaffin ‘yan majalisa na shekarar 2026 da aka gudanar a birnin Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A jawabinsa, Gbajabiamila ya goyi bayan tsarin karba-karbar, yana mai cewa wannan tsari ne cike da hikima da adalci da aka tsara domin tafiyar da bambancin Najeriya, rage tashin hankali a siyasa, da kuma kare zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasa.
