Gwamnatin Nijeriya ta yi niyyar kera dukkan makami da ake buƙata a cikin gida nan da shekara biyu zuwa biyar masu zuwa.
Minista a ma’aikatar Tsaron kasar Bello Matawalle a yayin ƙaddamar da motar sulke ta soja DICON X-Shield da kuma wasu motocin sulke da aka kera a Nijeriya, ya ce gwamnatin Tinubu ta fara shimfiɗa tubalin dakatar da shigo abinda jami’an tsaro ke buƙata daga ƙasashen waje.
Jaridar Punch ta ruwaito Matawalle wanda Darakta Janar na DICON, Manjo Janar Babatunde Alaya ya wakilta, ya ce abin da ake gani a yanzu shi ne mataki na farko na babbar dabara da za ta kai ga cikakken shirin kera makamai a gida.
Ya ce nan da shekaru kaɗan Nijeriya za ta daina dogaro da ƙasashen waje domin samar da kayan tsaro, lamarin da zai samar da ayyukan yi, ya rage fitar da kuɗaɗen ƙasa waje, tare da bai wa Nijeriya damar fitar da makamai zuwa wasu ƙasashe.
