Rundunar ‘yan sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta shawarci ƙungiyar kwadago NLC da ta sake duba jadawalin zanga-zangar da ta shirya yi a ranar Talata, 3 ga Fabrairu 2026, bayan bayanan sirri sun nuna yiwuwar wasu ƙungiyoyi da ba na gwamnati ba, na kitsa yadda za su karkatar da zanga-zangar, lamarin da ka iya jefa jama’a cikin hatsari.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja SP Josephine Ade da ta aike wa kafafen yada labarai ciki hada DCL Hausa.
