Tsohon gwamnan Jihar Kaduna kuma jigo a jam’iyyar ADC, Malam Nasir El-Rufai, ya zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da hana shigar da tanadin tura sakamakon zabe kai tsaye ta yanargizo a cikin kudurin gyaran Dokar Zabe dagangan.
El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin 30 Minutes na Trust TV, inda ya ce matsalar ba ta fito daga sanatoci ba, illa daga shugabancin Majalisar.
A cewarsa, yawancin sanatoci na goyon bayan kudurin da Majalisar Wakilai ta amince da shi, wanda ke wajabta tura sakamakon zabe kai tsaye daga rumfunan zabe, amma shugabancin Majalisar Dattawa na dakile batun.
El-Rufai ya zargi jam’iyya mai mulki da tsoron sahihin zabe, yana mai cewa hakan ne ya sa ake kokarin barin damar sauya sakamako bayan an kada kuri’a.
Tsohon gwamnan ya kuma bayyana nadamarsa kan rashin halartar zanga-zangar da Peter Obi da sauran ‘yan adawa suka yi a Majalisar Tarayya, inda ya ce da yana Abuja da ya halarta.
