Babban hafsan sojin kasa na Nijeriya Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya ce gagarumar sadaukarwar da Nijeriya ta yi ne ya samar da daidaito da zaman lafiya a Liberia, lokacin da kasar ke fama da yakin basasa.
Waidi Shaibu ya bayyana haka ne a Liberia yayin bikin tunawa da ‘yan mazan jiya na kasar, kamar yadda sashen hulda da jama’a na rundunar sojin Nijeriya ya bayyana cikin wata sanarwa.
A cewar sa, Nijeriya ce ta dauki kaso mafi tsoka na nauyin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, a zamanin yakin.
Ya kuma jaddada kudurin gwamnatin Nijeriya wajen ci gaba da karfafa alaka da kasar musamman ta fuskar tsaro.
