Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta Nijeriya FRSC ta kori jami’anta 43 kan samun su da aikata laifukan da suka shafi saba wa ka’idojin aiki.
Wata sanarwa da jami’in wayar da kai na hukumar Olusegun Ogungbemide ya fitar, ta nuna cewa an kori 31 daga cikin jami’an ne saboda laifin barin wurin aiki ba bisa ka’ida ba, biyar saboda aikata wasu munanan laifuka, sai bakwai saboda laifukan da suka shafi aikin sintiri.
Babban kwamandan FRSC Shehu Muhammad, ya bayyana daukar matakin a matsayin wata hanya ta tsaftace aikin hukumar, yana mai cewa ba za ta lamunci duk wani nau’i na rashin da’a ko saba dokar aiki ba.
