Tsohon ɗan takarar shugabacin Nijeriya Peter Obi, ya yi kira ga ’yan kasar da su kasance masu sa ido sosai a zaɓen 2027, yana jaddada cewa dole ne kowace ƙuri’a a kirga ta, tare da yin gargaɗi ga duk wanda zai yi ƙoƙarin kawo cikas ga sahihin zaɓe.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Obi ya wallafa saƙon ne a shafinsa na X, inda ya bukaci masu jefa ƙuri’a su tsaya a rumfunan zaɓe bayan sun kaɗa ƙuri’unsu domin su shaida an ƙirga da kuma tura sakamakon zuwa hukumomi.
Obi ya ce halartar jama’a da sa ido a rumfunan zaɓe na da matuƙar muhimmanci wajen kare dimokiraɗiyya da hana maguɗin zaɓe.
