Hukumar ICPC mai yaki da ayyukan rashawa a Nijeriya ta fara bibiyar ayyuka 64, na ‘yan majalisa da aka kiyasta kuɗinsu kimanin Naira biliyan 21.6 a jihar Sokoto.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa wannan bincike na karkashin mataki na 8 a shirin ICPC na bibiyar ayyukan ‘yan majalisa wanda ake aiwatarwa a jihohi daban-daban na ƙasar.
Shugaban tawagar binciken, Aminu Bala, ya bayyana cewa za su duba ayyuka a fannoni daban-daban kamar kiwon lafiya, ilimi, samar da ruwan sha, noma, da kuma lantarki.
A cewarsa, sun gano kura-kurai a wasu ayyuka da aka aiwatar a Kalambaina da Gwuiwa a karamar hukumar Wamakko, da kuma Mabera da Mana a Sokoto ta Kudu.
