DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ma’aikatan lafiya sun tafi yajin aikin gargadi na kwanaki 7

-

Likitoci

Kungiyoyin hadin gwiwa na bangaren lafiya JOHESU da kwararrun ma’aikatan lafiya sun sanar da fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai, wanda zai fara da tsakar daren Juma’a 25 ga Oktoba, 2024.

Matakin ya biyo bayan cikar wa’adin kwanaki 15 da aka baiwa gwamnatin tarayya a baya kan bukatun da ma’aikatan lafiyar ke nema.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, shugaban kungiyar JOHESU na kasa, Kabiru Minjibir, ya bayyana muhimman bukatun kungiyar, wadanda suka hada da aiwatar da tsarin tsarin albashi mai tsoka ga ma’aikatan lafiya,da kuma sake fasalin shekarun ritaya ga ma’aikatan kiwon lafiya,sauran buƙatun sun haɗa da biyan alawus-alawus ɗin ma’aikatan kiwon lafiya.   

Yajin aikin na gargadin dai na iya kawo cikas ga ayyukan kiwon lafiya a fadin kasar, musamman a manyan cibiyoyin kiwon lafiyar al’umma.

Yajin aikin na baya-bayan nan da kungiyar ta JOHESU ta yi ya biyo bayan tattaunawa da gwamnatin tarayya ta yi, wanda da yawa daga cikinsu ba a samu sakamako mai kyau ba.Kungiyar dai ta ba da shawarar inganta yanayin aiki ga kwararrun masana kiwon lafiya, musamman dangane da gudummawar da suka bayar yayin afkuwar cutar COVID-19.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kwamishinan Jigawa ya mayar da rarar Naira miliyan 301 daga kudaden da aka ware don shirin ciyar da al’umma a watan Ramadan

Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa, Alhaji Auwalu Danladi Sankara, ya mayar da Naira miliyan 301 zuwa baitul malin jihar, daga cikin Naira biliyan...

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta karɓi wasikun kulla kawance daga sabbin jakadun ƙasashe 8

A ranar Juma’a, 9 ga Mayu, 2025, fadar gwamatin ta Jamhuriyar Nijar ta karɓi sabbin jakadun daga jakadun ƙasashen duniya guda takwas. Inda shugaban mulkin sojin...

Mafi Shahara