Kungiyar Hausawa mazauna Jihar Rivers ta bayyana cewa mambobinta hudu sun hadu da ajalinsu a yayin zanga-zangar da ta gudana a karshen makon da ya gabata, wadda aka ce ta shafi ‘yan Arewa a Kasuwar Oil Mill da ke yankin Rumuokwurusi a Port Harcourt.
Shugaban Kungiyar Hausawan Jihar Rivers, Alhaji Musa Saidu, ne ya bayyana hakan a ranar Talata lokacin da ya jagoranci wasu shugabannin Arewa zuwa kasuwar domin duba halin da ake ciki, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Ya kuma ce an wawashe tare da lalata shaguna da dama mallakin ‘yan kasuwar Arewa a lokacin tashin hankalin
