Sanannen dan kasuwa a Afrika Aliko Dangote, ya ce ana sa ran darajar naira za ta iya dagawa zuwa kusan ₦1,100 kan dala ɗaya a shekarar 2026, idan sauye-sauyen tattalin arziƙi da rage dogaro da shigo da kaya daga waje suka ci gaba da aiki yadda ya kamata.
Dangote ya faɗi hakan ne a lokacin ƙaddamar da wani shiri da aka kaddamar kan masana’antu na 2025, inda ya jaddada muhimmancin ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida domin rage buƙatar dala daga waje.
Ya bayyana cewa farfadowar naira da ake gani a ‘yan makonnin nan na da alaƙa da manufofin gwamnati na ƙarfafa masana’antu da kuma rage shigo da kayayyaki, musamman man fetur da wasu muhimman kayayyaki.
