Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya bukaci ‘yan kasar da su rika sanya Shugaba Bola Ahmed Tinubu a cikin addu’o’insu yayin da Musulmi ke gudanar da Ramadan, Kiristoci kuma ke azumin Lent.
A cikin wata sanarwa da mataimakinsa kan harkokin yaɗa labarai ya fitar, Shettima ya ce wannan lokaci mai tsarki na ibada ya kamata ya zama dama ta roƙon Allah ya bai wa Tinubu hikima, ƙarfi da hangen nesa domin tafiyar da al’amuran ƙasa yadda ya dace, musamman a wannan lokaci na sauye-sauyen manufofi da ƙalubalen shugabanci.
Ya jaddada cewa haɗuwar Ramadan da Lent a lokaci guda dama ce ta haɗa kai wajen yin addu’a domin shugabanci nagari, zaman lafiya da kwanciyar hankali.
