AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar ‘yan sandan kasar a matsayin IGP na 23.
A cewar fadar shugaban Nijeriya, zai gudanar da aikin ne a matsayin muƙaddashi har sai an tantance shi kamar yadda tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Takaitaccen Tarihin Sa
- Haihuwa: An haife shi a ranar 13 ga Afrilu, 1966, a Jihar Legas.
- Karatu: Yana da digiri a fannin Turanci (English Education) daga Jami’ar Jihar Legas (LASU). Sannan yana da digiri na biyu (Masters) guda biyu: daya a fannin Gudanarwa (Public Administration) daga Jami’ar Adekunle Ajasin, daya kuma a fannin Kimiyyar Laifuka (Criminology) daga LASU.
- Fannin Kwarewa: Ya halarci kwasa-kwasai da dama a gida da waje kan yaki da fataucin makamai, zambar intanet (internet fraud), da binciken kimiya na gano masu laifi (forensics).
- Disu ya shiga aikin dan sanda ne a shekarar 1992 a matsayin babban jami’i (Cadet ASP), inda ya samu horo a Makarantar Horon ‘Yan Sanda ta Wudil da ke Jihar Kano.
- Ga wasu daga cikin manyan mukaman da ya rike:
- AIG FCID Alagbon: Kafin nadinsa na yanzu, shi ne Mataimakin Sufeto Janar mai kula da sashin binciken manyan laifuka a Legas.
- Kwamishinan ‘Yan Sanda (CP): Ya taba rike rundunar ‘yan sanda ta Abuja (FCT) a 2024 da ta Jihar Rivers a 2023.
- Kwamandan IRT: Shi ne ya gaji Abba Kyari a matsayin shugaban tawagar gano masu laifi (Intelligence Response Team) a shekarar 2021.
- Kwamandan RRS: Ya taba jagorantar rundunar gaggawa (Rapid Response Squad) ta Jihar Legas.
- Babban Jami’i ga IGP: Ya taba zama Principal Staff Officer ga tsohon IGP Egbetokun.
Me Ya Faru da IGP Kayode Egbetokun?
An nada Egbetokun ne a matsayin wanda ya gaji Usman Alkali Baba. Ko da yake ya kamata ya yi ritaya a ranar 4 ga Satumba, 2024 (lokacin da ya cika shekaru 60), sai dai gyaran da aka yi wa dokar ‘yan sanda ya ba shi damar ci gaba da wa’adin shekaru hudu, wanda hakan zai kai shi har zuwa watan Oktoba, 2027.
Sai dai, ya yi murabus sakamakon wasu dalilai, inda fadar shugaban Nijeriya ta sanar da nadin Disu domin ya jagoranci rundunar yan sandan Nijeriya.
