Rundunar ‘yan sanda a jihar Sokoto ta tabbatar da cewa mutum daya ya rasa ransa yayin da mutane biyar suka shiga hannun ‘yan bindiga a kauyen Mallamawar Yari da ke karamar hukumar Rabah.
Mai magana da yawun rundunar, Ahmed Rufai, ya ce harin ya faru ne a daren Asabar, inda maharan suka kai farmaki garin.
Jaridar Punch ta ambato ya kuma musanta jita-jitar cewa maharan sun sanya hijabi domin boye kansu.
‘Yan sanda sun ce wadanda aka sace sun hada da mata uku da maza biyu, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da kokarin ceto su tare da kamo wadanda suka aikata laifin.
