Wani jigo a jam’iyyar ADC, Dele Momodu, ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ba shi da karfin kudin da zai iya fafatawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Momodu ya yi wannan bayani ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.
A cewarsa, yanayin siyasar Najeriya na nuna alamun komawa tsarin jam’iyya guda, inda ya kwatanta halin da ake ciki da lokacin mulkin tsohon shugaban soja Sani Abacha.
Momodu ya kuma karyata rade-radin cewa yana shirin cin amanar Atiku, yana mai cewa bai taba halartar wani taro a boye ba ba tare da sanin Atiku ba.
Sai dai ya bayyana cewa dangantakarsa da Tinubu ta fi kusa fiye da ta Atiku, lamarin da ya sa wasu ke zargin cewa yana iya zama dan leken asirin Tinubu a cikin bangaren adawa.
