Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaWike ya soki yunkurin Gwamnan Bauchi Bala na barin PDP

Wike ya soki yunkurin Gwamnan Bauchi Bala na barin PDP

Kasa da sa’o’i 24 bayan gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, tare da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, sun kai ziyara fadar gwamnatin Bauchi a ranar Laraba.

An hango shugabannin biyu na shiga fadar gwamnatin, inda suka yi wata ganawa ta sirri da Gwamna Bala Mohammed.
Bayan kammala taron, babu daya daga cikin bangarorin da ya yi wa manema labarai bayani.

Ana sa ran gwamnan zai sanar da jam’iyyar da zai koma a yau Alhamis din nan.

Wannan na zuwa ne yayin da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya soki gwamnan kan rashin daidaito a matsayinsa.
Majiyoyi daga fadar gwamnatin sun ce ziyarar na iya nasaba da kokarin shawo kan gwamnan ya sake tunani kan shirin komawa ADC, maimakon haka ya hade da APC.

Wannan ci gaba na zuwa ne kwana guda bayan Gwamnan Bala, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar gwamnonin PDP, ya karbi bakuncin wata tawagar jam’iyyar ADC karkashin jagorancin tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal.

Da yake magana da manema labarai bayan taron na ranar Talata, gwamnan ya danganta shirin sauya shekar nasa da rikicin da ke ci gaba da faruwa a cikin jam’iyyar PDP, yana mai cewa kokarin sulhu bai yi nasara ba.

Ya ce, “Mun tsinci kanmu a cikin wani mawuyacin hali. Na yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da sulhu, amma hakan bai yi nasara ba.”

A yayin da yake duba ayyukan gina hanyoyi a Abuja a ranar Laraba, Wike ya zargi Gwamnan Bala da cewa a baya ya taba kokarin yin sulhu da APC, inda ya tuna da wata tafiya da gwamnan ya kai Port Harcourt a shekarar 2022, inda ake zargin ya nemi goyon bayan Bola Tinubu, kafin daga bisani ya koma goyon bayan dan takarar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar.

Ya ce, “Abin kunya ne sosai. Yanzu ys fada maka magana, da safe ya sauya ta, da rana kuma sai ya fadi wani daban.”

“Bala, muna farin ciki sosai da ka bayyana wa ‘yan Nijeriya wanene kai—cewa ba ka da tsayayyiyar matsaya,” in ji Wike.

Wike ya kuma yi magana kan rikicin cikin gida na PDP, yana mai cewa jam’iyyar na nan daram duk da kalubalen shari’a da take fuskanta.
Ya soki bukatar da Gwamna Bala ya gabatar na neman mukamin sakataren jam’iyyar daga abin da ya kira matsayi mai rauni.
Ya ce, “An riga an kayar da kai, ka yi rashin nasara. Kana magana ne daga matsayi mai rauni, sannan kuma kana son neman mukamin sakataren jam’iyya? Hakan ba daidai ba ne.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata