Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, domin kawo ayyukan ci gaba da tallafin gwamnatin tarayya zuwa jihar.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar, bayan dawowar gwamnan Kano daga Abuja.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen samar da romon dimokuraɗiyya ga al’umma, musamman a muhimman fannoni kamar ci gaban tattalin arziki, abubuwan more rayuwa da walwalar jama’a.
