Wasu ‘yan ta’adda sun kai hari a ƙauyen Ariko da ke karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna, inda suka kai farmaki majami’u biyu a lokacin bukukuwan Easter, suka halaka aƙalla mutane bakwai tare da yin garkuwa da wasu.
Jaridar Punch ta rawaito cewa harin ya faru ne a safiyar Lahadi, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici, wakilin mazabar Awon, Mark Bawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce majami’un da abin ya shafa sun hada da First ECWA Church da St. Augustine Catholic Church da ke Ariko.
A cewarsa, maharan sun zo da yawa, suka kewaye yankin sannan suka fara harbe-harbe kan masu ibada, inda suka halaka mutane da dama tare da sace wasu zuwa cikin daji.
