Monday, April 6, 2026
HomeKasuwanciFarashin Kayan Abinci a Nijeriya 30.03.2026 – 05.04.2026

Farashin Kayan Abinci a Nijeriya 30.03.2026 – 05.04.2026

A mako na 14 na shekarar 2026, wato daga 30.03.2026 – 05.04.2026, DCL Hausa ta lura da karin farashin wasu muhimman kayan abinci a sassan Najeriya, musamman shinkafa yar gida da taliya a wasu kasuwanni. Sai dai farashin wake da wasu nau’in shinkafa ya tsaya cak a wasu wurare, yayin da aka samu ragi kaɗan a wasu kasuwanni.

Abubuwan da suka fi daukar hankali a wannan makon

  • Mafi girman kari: Shinkafa yar gida a Dawanau, Kano (+N20,000)
  • Mafi girman ragi: Taliya a Mile 12, Legas (-N1,000)
  • Kasuwar da ta fi tsada a wake: Mile 12, Legas (N110,000)
  • Farashin da bai sauya ba: Shinkafar bature a Giwa, Kaduna (N75,000)

Abin Lura:
Farashin da ke cikin wannan jadawali na iya sauyawa daga dan kasuwa zuwa dan kasuwa ko daga rana zuwa rana. DCL Hausa na tattaro farashin ne daga zababbun manyan kasuwanni domin sanar da jama’a da hukumomi gami da kungiyoyi halin da kasuwanni ke ciki a kowane mako.

Kayan masarufi Kasuwa Farashin mako na 14 Farashin mako na 13 Banbanci Matsayi
Shinkafa yar gida (Jamila) Dawanau, Kano N120,000 N100,000 +N20,000 Ya tashi
Shinkafa yar gida Mai’adua, Katsina N105,000–N110,000 N100,000 +N5,000 zuwa +N10,000 Ya tashi
Shinkafa yar gida Zamani, Adamawa N95,000 N90,000 +N5,000 Ya tashi
Shinkafa yar gida Giwa, Kaduna N90,000–N100,000 N90,000–N100,000 Babu canji Bai sauya ba
Shinkafa yar gida Mile 12, Legas N90,000 N90,000 Babu canji Bai sauya ba
Shinkafa yar gida Saminaka, Kaduna N100,000 N98,000 +N2,000 Ya tashi
Shinkafar bature (India/Thailand) Giwa, Kaduna N75,000 N75,000 Babu canji Bai sauya ba
Shinkafar bature (India/Thailand) Dawanau, Kano N65,000 N62,000 +N3,000 Ya tashi
Shinkafar bature (India/Thailand) Mile 12, Legas N65,000 N65,000 Babu canji Bai sauya ba
Shinkafar bature (India/Thailand) Zamani, Adamawa N65,000–N70,000 N65,000–N70,000 Babu canji Bai sauya ba
Wake Mile 12, Legas N110,000 N110,000 Babu canji Bai sauya ba
Wake Zamani, Adamawa N85,000–N90,000 N80,000–N90,000 Ya dan tashi Ya tashi
Wake Mai’adua, Katsina N83,000–N85,000 N83,000–N85,000 Babu canji Bai sauya ba
Wake Saminaka, Kaduna N70,000 N75,000 -N5,000 Ya sauka
Wake Giwa, Kaduna N70,000–N75,000 N70,000–N75,000 Babu canji Bai sauya ba
Wake Dawanau, Kano N75,000–N80,000 Ba a fayyace ba
Masara Zamani, Adamawa N32,000–N33,000 N30,000 +N2,000 zuwa +N3,000 Ya tashi
Masara Mile 12, Legas N42,000 N40,000 +N2,000 Ya tashi
Masara Dawanau, Kano N30,000–N32,000 N30,000–N32,000 Babu canji Bai sauya ba
Masara Giwa, Kaduna N27,000–N29,000 N27,000–N29,000 Babu canji Bai sauya ba
Masara Saminaka, Kaduna An ce ita ce mafi rahusa, amma ba a bayar da adadi ba
Masara Mai’adua, Katsina N33,000 Ba a fayyace ba
Taliya Zamani, Adamawa N14,000 N13,500 +N500 Ya tashi
Taliya Kano N14,000 N13,500 +N500 Ya tashi
Taliya Mile 12, Legas N15,000 N16,000 -N1,000 Ya sauka
Spaghetti Giwa, Kaduna N12,000 N12,000 Babu canji Bai sauya ba
Spaghetti Saminaka, Kaduna N12,000 N12,000 Babu canji Bai sauya ba
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata