Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta bayyana cewa Najeriya na asarar kusan ton miliyan 38 na abinci a duk shekara, mafi yawa a nahiyar Afirka.
Mataimakin jakadan EU a Najeriya da ECOWAS, Zissimos Vergos, ya ce wannan matsala na da illa ga tattalin arziki, muhalli da kuma yaƙi da yunwa.
Ya bayyana cewa duk lokacin da aka zubar da abinci, ana kuma lalata albarkatun da aka yi amfani da su wajen samar da shi, kamar ruwa, makamashi da ƙoƙarin ɗan Adam.
EU tare da gwamnatin tarayya da kuma United Nations Industrial Development Organization sun buƙaci a ɗauki matakan gaggawa domin rage asarar abinci da inganta amfani da albarkatu yadda ya kamata.
Rahotanni sun nuna cewa a duniya baki ɗaya, kusan ton biliyan ɗaya na abinci ake ɓatawa a shekarar 2022, wanda ya kai kusan kashi 20 na abincin da ake samarwa.
EU ta kuma jaddada cewa asarar abinci na taka rawa wajen dumamar yanayi, inda take haifar da kusan kashi 10 na hayakin da ke dumama duniya.
A nasa ɓangaren, Ministan muhalli, Balarabe Lawal, ya ce gwamnati na ɗaukar matakai domin rage asarar abinci, ciki har da shirye-shiryen rage ɓarnar abinci a manyan kasuwanni.
Haka kuma, wakilin hukumar MDD a Najeriya ya jaddada muhimmancin inganta tsarin samar da abinci domin rage asara da ƙarfafa tattalin arziki.
EU ta ba Najeriya shawarwari uku, da suka haɗa da inganta hanyoyin karkara da ajiya, ƙarfafa sarrafa kayan amfanin gona, da kuma koyar da al’adun rage ɓarna tun daga makarantu.
