Tuesday, April 7, 2026
HomeSiyasaYusuf Buhari ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a 2027

Yusuf Buhari ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a 2027

Ɗan marigayi tsohon shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, wato Yusuf Buhari, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai.

A cikin wata wasiƙa da aka ruwaito ya aike wa masu ruwa da tsaki a ranar 3 ga Afrilu, Yusuf ya ce yana da burin bayar da gudunmawa wajen inganta shugabanci da kawo ci gaba ga al’umma.

Tun da farko dai wasu jiga-jigan jam’iyyar APC sun nuna goyon bayansu gare shi domin tsayawa takarar wakilcin mazabar Daura/Sandamu/Mai’Adua.

Sai dai rahoton jaridar Daily Trust ya ambato wasu masu ruwa da tsaki a yankin sun nuna adawa da abin da suka kira yunƙurin kakabawa jam’iyya ‘yan takara, suna mai cewa za su ci gaba da bin tsarin dimokuraɗiyya na jam’iyyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata