Kungiyar ATM Gwarzo ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, tare da manufofin gwamnatinsu na Renewed Hope da Kano First.
Hakan na kunshe ne cikin Sanarwar da shugaban kwamitin kungiyar, Hon. Magaji Shehu Lambu, ya sanya wa hannu a ranar 7 ga Afrilu, 2026.
A cikin sanarwar, kungiyar ta kuma bukaci Abdullahi Tijjani Gwarzo da ya amsa kiraye-kirayen magoya bayansa tare da tsayawa takarar Sanatan Kano ta Arewa a babban zaben shekarar 2027.
Kungiyar ta jaddada cewa za ta ci gaba da bayar da cikakken goyon baya tare da shirye-shiryen tattara jama’a a dukkan matakai domin ganin an cimma wannan buri.
