Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiNimet ta yi hasashen kwallewar rana na kwanaki uku a Nijeriya

Nimet ta yi hasashen kwallewar rana na kwanaki uku a Nijeriya

 

Hukumar kula da hasashen yanayi ta Nijeriya, Nimet, ta yi hasashen samun kwallewar rana da gajimare tare da yiwuwar tsawa da ruwan sama a sassa daban-daban na ƙasar daga Litinin zuwa Laraba.

A rahoton da hukumar ta fitar a Abuja, ta bayyana cewa yankin Arewa zai fuskanci hasken rana tare da gajimare a safiya, yayin da ake sa ran tsawa mai ɗauke da ruwan sama a wasu sassan jihar Taraba daga baya a rana ta fito.

A yankin Arewa ta Tsakiya kuwa, ana hasashen yanayin gajimare da ɗan hasken rana da safe, sannan daga baya a samu tsawa da ruwan sama a wasu sassan jihar Kogi da Benue.

Jaridar Daily Nigerian ta ce a yankin Kudu, rahoton ya ce za a fara da gajimare da yiwuwar tsawa da safe a Akwa Ibom da Cross River, kafin daga baya a ruwan sama ya bazu a yawancin yankin da rana.

A ranar Talata, NiMet ta ce za a ci gaba da samun rana da gajimare a Arewa, tare da yiwuwar tsawa a wasu sassan Kaduna da Taraba da safe, sannan daga baya a samu matsakaicin ruwan sama a Adamawa, Borno, Gombe, da Bauchi.

A Arewa ta Tsakiya kuma, ana sa ran samun tsawa hade da ruwan sama a yankunan Plateau, Nasarawa, da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

A yankin Kudu, ana sa ran tsawa da ruwan sama da zai mamaye yawancin yankin a ranar.

Sai kuma a ranar Laraba, rahoton ya nuna cewa za a samu tsawa da ruwan sama a Kaduna, Taraba, Adamawa, Borno, da Gombe.

A yankin Kudu kuwa, Lagos, Ogun, Osun, Ondo, Delta, Bayelsa, Cross River, da Akwa Ibom za su fuskanci tsawa da ruwan sama tun daga safe.

Hukumar ta gargadi jama’a da su ɗauki matakan kariya, musamman saboda yiwuwar iska mai ƙarfi kafin saukar ruwan sama, tare da tabbatar da ɗaure abubuwan da iska ka iya ɗauka.

Haka kuma, ta shawarci mutane da su guji tuki a lokacin ruwan sama mai ƙarfi, su cire kayan lantarki daga soket, sannan su nisanci manyan bishiyoyi domin kauce wa hatsari.

NiMet ta ƙara da cewa yanayin zafi zai ci gaba da kasancewa mai yawa, don haka ta buƙaci jama’a su rika sanya tufafin da ba shi da nauyi, su zauna a wurare masu iska, tare da shan ruwa sosai.

Har ila yau, ta shawarci kamfanonin jiragen sama da su rika neman rahotannin yanayi na musamman daga hukumar domin tsara zirga-zirgarsu yadda ya dace.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata