Tuesday, April 7, 2026
HomeWasanniMaguire ya sabunta kwantiraginsa da Man United

Maguire ya sabunta kwantiraginsa da Man United

Jagoran ‘yan wasan Manchester United Harry Maguire ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi wanda zai ba shi damar ci gaba da zama a ƙungiyar har zuwa watan Yuni na shekarar 2027.
Fabrizio Romano ya ruwaito cewa tsohon dan wasan na Ingila mai shekaru 33, ya kusa kammala zama a kungiyar ƙarshen a kakar ta bana amma ya amince da kulla sabuwar yarjejeniya domin ci gaba da zamansa a Manchester United.
Jaridar Punch ta ambato Maguire, wanda ya koma United daga Leicester City a shekarar 2019 kan kuɗi kusan fam miliyan 80, ya buga wasanni 266 inda ya zura kwallaye 17 a ƙungiyar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata