Likitoci a Ingila sun sake tsunduma yajin aiki karo na 15 cikin shekaru uku, sakamakon sabani tsakaninsu da gwamnati kan albashi da yanayin aiki.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana cewa, likitocin sun fara yajin aikin na tsawon kwanaki shida duk da cewa sun samu karin albashi na kashi 28.9 cikin dari a cikin shekaru uku da suka gabata.
Ministan Lafiya na Birtaniya, Wes Streeting, ya soki matakin ƙungiyar likitocin na ƙin amincewa da karin kashi 4.9 cikin dari da gwamnati ta bayar, yana mai cewa likitocin sun fi kowa samun karin albashi a ma’aikatan gwamnati.
Sai dai ƙungiyar likitocin na neman a dawo da albashinsu zuwa matakin da yake a shekarar 2008, suna masu cewa hauhawar farashi ya rage musu ƙimarsa sosai.
