Tuesday, April 7, 2026
HomeSiyasaAtiku ya gargadi Tinubu kan raba tallafin taliya da shinkafa ga masu...

Atiku ya gargadi Tinubu kan raba tallafin taliya da shinkafa ga masu zabe

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya gargaɗi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu cewa dogaro da rabon kayan tallafi ba zai tabbatar masa da sahihanci ko nasara a zaɓen 2027 ba.

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Talata, inda ya jaddada cewa rabon kayayyaki irin su shinkafa, taliya da Indomie ba su isa su gina amincewar jama’a ba.

A cewarsa, duk da cewa irin waɗannan matakai na iya rage raɗaɗin rayuwa na ɗan lokaci, ba za su iya tantance sakamakon zaɓe ko maye gurbin sahihiyar goyon bayan jama’a ba.

Jaridar Punch ta ruwaito shi ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da ƙoƙarin ƙarfafa ikonta tare da rage fadin dimokuraɗiyya, duk da cewa tana da rinjaye a fagen siyasa.

Atiku ya ce akwai alamun fargaba daga bangaren gwamnati, musamman yadda ake kallon ‘yan adawa da masu zaɓe, duk da yawan goyon bayan da jam’iyyar mai mulki ke samu daga shugabanni.

Haka kuma, ya nuna damuwa kan abin da ya kira ƙoƙarin raunana jam’iyyun adawa ta hanyar rikice-rikicen cikin gida da kuma tsoma bakin kotuna.

Ya kuma soki abin da ya bayyana a matsayin amfani da ƙarfin gwamnati wajen matsa lamba ga ‘yan adawa, ciki har da bayar da umarnin tsare wasu ba tare da bin ƙa’ida ba.

Atiku ya yi gargadin cewa idan aka ci gaba da irin wannan tafiya, Najeriya na iya fadawa cikin tsarin jam’iyya ɗaya, inda zaɓe zai kasance a rubuce kawai ba tare da sahihin gasa ba.

Daga ƙarshe, ya buƙaci ‘yan Najeriya da su kasance cikin shiri da lura gabanin zaɓen 2027, yana mai cewa dole ne shugabanci ya kasance bisa ra’ayin jama’a, ba tare da danniya ko amfani da iko ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata