Thursday, April 9, 2026
HomeSiyasaADC ta kafe kan ci gaba da shirya taronta duk da rikicin...

ADC ta kafe kan ci gaba da shirya taronta duk da rikicin shugabanci

Jam’iyyar ADC ta ce za ta ci gaba da shirye-shiryen tarukanta na ƙasa da na jihohi duk da rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar.

Ɗaya daga cikin jagororin jam’iyyar, Ralph Nwosu, ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi, inda ya ce jam’iyyar ba za ta bari rikicin ya dakatar da shirinta na zaɓen 2027 ba.

Ya ce sun riga sun miƙa jadawalin tarukansu ga Hukumar Zaben Nijeriya INEC, kuma bisa doka suna da damar ci gaba da gudanar da su ko da hukumar ba ta halarta ba.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito Nwosu ya ƙara da cewa tuni aka fara gudanar da zaɓukan cikin gida, yayin da babban taron ƙasa (convention) da aka shirya zai gudana domin tabbatar da dukkan matakan da aka ɗauka, ciki har da zaɓen ‘yan takara.

Sai dai rikicin ya ƙara tsananta ne bayan INEC ta ce ba za ta amince da shugabancin ɓangaren David Mark ko na Nafiu Bala ba, har sai kotu ta yanke hukunci kan wanda ya dace.

Hukumar ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da bin halin da ake ciki kafin fara shari’ar a kotu.

Rikicin ya samo asali ne bayan murabus ɗin da Nwosu ya yi a shekarar 2025, wanda ya buɗe ƙofa ga sabon shugabanci, yayin da Bala ke ikirarin cewa shi ne ya kamata ya gaji kujerar.

A halin yanzu dai, jam’iyyar da wasu manyan ‘yan siyasa sun gudanar da zanga-zanga a Abuja, suna zargin gwamnati da ƙoƙarin mayar da Najeriya ƙasa mai bin tsarin jam’iyya ɗaya.

Sai dai fadar shugaban ƙasa ta musanta zargin, tana mai cewa babu wani shiri na hana sauran jam’iyyu shiga zaɓe, tare da jaddada cewa duk jam’iyyu na da damar tsayar da ‘yan takara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata