Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Sunday Dare, ya musanta zargin cewa jam’iyyar na ƙoƙarin zama ita kaɗai a takarar zaɓen 2027.
Dare ya bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce babu wani shiri a ɓoye ko a bayyane na hana sauran jam’iyyu shiga zaɓe.
Ya ce akwai jam’iyyu 21 da hukumar zaben Nijeriya INEC ta yi wa rijista, kuma kowacce na da damar tsayar da ‘yan takara.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan kakakin jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya zargi APC da haddasa rikice-rikice a jam’iyyun adawa domin rage musu ƙarfi kafin zaɓen 2027.
Sai dai Dare ya yi watsi da zargin, yana mai cewa matsalolin da ke cikin ADC na cikin gida ne, kuma jam’iyyar APC ba ta da hannu a ciki.
Ya kuma ce zanga-zangar da ADC ta gudanar a gaban INEC na nuna cewa akwai cikakkiyar ‘yancin siyasa a ƙasar.
Dare ya ƙara da cewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bai damu da adawa ba, domin yana mai da hankali ne kan shugabanci da tafiyar da harkokin ƙasa.
A ƙarshe, ya buƙaci ADC da sauran jam’iyyun adawa su bi hanyar doka wajen warware matsalolinsu maimakon zargin gwamnati.
