Akalla mutum takwas sun rasa rayukansu sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai a ƙauyen Mbwelle da ke ƙaramar hukumar Bokkos a jihar Filato.
Rahotannin da gidan talabijin na Channels ya tattaro sun ce maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 11 na dare, inda suka riƙa harbe-harbe na kusan awa guda.
Dukkan mutanen da aka yi ajalinsu ‘yan gida ɗaya ne, yayin da wasu uku suka jikkata, sannan har yanzu ana neman wasu da suka ɓace.
Shugaban ƙaramar hukumar Bokkos, Samuel Amalau, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai cewa hare-haren na baya-bayan nan sun sake tayar da hankali a yankin.
A nasa ɓangaren, kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar, Alfred Alabo, ya ce ana ci gaba da bincike kan lamarin, kuma za a fitar da cikakken bayani nan gaba.
