DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
HomeLabarai‘Yan Nijeriya na bukatar mataki kan wadanda ake zargi da hannu a...

‘Yan Nijeriya na bukatar mataki kan wadanda ake zargi da hannu a ta’addanci

A ranar Asabar, Gwamnatin Nijeriya ta fitar da jerin sunayen mutane 48 da kamfanoni 12 da ake zargi da hannu wajen daukar nauyin ayyukan ta’addanci, lamarin da ya janyo kiraye-kiraye daga ‘yan kasar da masana tsaro na bukatar a dauki mataki cikin hanzari domin tabbatar da gaskiya da adalci.

Jaridar Punch ta ambaci wasu fitattun mutane da ake zargi ke ɗaukar nauyin ta’addanci a manyan kungiyoyi ‘yan ta’adda a yammacin Afrika.

A cewar rahoton, wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da gwamnati ke ikirarin samun nasara a shari’o’in ta’addanci, inda ta samu hukunci a kan mutane 386 daga cikin shari’o’i 508 da aka gabatar, duk da cewa hare-hare na ci gaba tsananta a jihohi da dama.

Masana harkokin tsaro sun jaddada cewa fitar da sunaye kadai bai wadatar ba, sai an dauki matakai kamar cafke wadanda ake zargi, da kuma gurfanar da su a gaban kotu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata