DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jigo a jam’iyyar PDP Bode George ya ce shugaban riko na Rivers bai da hurumin naɗa muƙamai

-

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Olabode George, ya gargadi shugaban riko na jihar Ribas, Admiral Ibok-Ete Ibas mai ritaya, kan nade-naden da yake yi a kwanan nan da kuma sake fasalin hukumomin jihar.
Bode George ya bayyana hakan a matsayin abinda ya saba doka da kuma yiwuwar yin da na sani a gaba. 
Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da aya fitar yau Jumu’a, inda ya bukaci Ibas da ya mutunta kundin tsarin mulki da bin doka da oda. 
Jigon na PDP ya kuma yi soka kan shugabannin rikon kwarya na kananan hukumomi 23 da ya naɗa, duk kuwa da umarnin da kotu ta bayar na haramta irin wadannan ayyuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatin Kano ta ware naira miliyan 99 domin rigakafin cutar mahaukacin kare

Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe Naira miliyan 99 domin fara shirin rigakafin cutar mahaukacin kare (rabies), inda ake sa ran yi wa akalla...

Wike ya koka kan ƙarancin masu fitowa zabe a Abuja

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana gamsuwarsa kan yadda ake gudanar da zaɓen kananan hukumomi cikin lumana a fadin Abuja, duk da...

Mafi Shahara