Kimanin likitoci 16,000 ne suka bar Nijeriya zuwa kasashen waje a cikin shekaru biyar zuwa bakwai da suka gabata.
Ministan lafiya Farfesa Muhammad Ali Pate ne ya bayyana hakan a Abuja yayin taron shekara-shekara na karawa juna sani na kungiyar Likitoci ta Afirka, wanda kungiyar likitoci ta Najeriya gudanar.
Ya ce balaguron da likitocin ke yi daga ƙasar bai rasa nasaba da damarmakin dake akwai a can da yanayin aiki da horo kazalika da yanayin bincike a ƙasashen wajen.
