Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiKungiyar matan 'yan sanda ta rabawa zawarawa awaki kusan 150 don inganta...

Kungiyar matan ‘yan sanda ta rabawa zawarawa awaki kusan 150 don inganta rayuwar su

Kungiyar
matan jami’an ‘yan sandan Nijeriya reshen jihar Kano, ta raba awaki 137 ga
matan da mazajensu suka mutu da kuma marasa galihu, domin bunkasa rayuwarsu

Hakan
dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan
sandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a Kano.

Shugabar ƙungiyar
Aisha Gumel wacce kuma ita ce uwargidan kwamishinan ‘yan sandan jihar, ta ce
matakin wani aiki ne na yau da kullun na tallafawa iyalan ma’aikatan da suka
mutu da waɗanda sukai ritaya da sauran marasa galihu a cikin al’umma.

Aisha
ta gabatar da takardar shaidar koyon sana’o’i ga ‘yan kungiyar sama da 100 da
suka samu horo tare da daukar nauyin fara sana’o’i daban-daban daga kungiyar.

 

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata