Wata babbar kotu a birnin tarayya ta yi watsi da karar da bangaren jam’iyyar NNPP mai littafi suka shigar, inda suke kalubalantar sahihancin shugabancin jam’iyyar karkashin Dr Boniface Aniebonam, da shugaban jam’iyyar na kasa, Dr. Agbo Major, suna masu bukatar a dakatar da su Boniface daga shirya babban taron jam‘iyya da sauran ayyukan jam‘iyya. Jaridar Punch ce ta ruwaito wannan labari a Juma‘ar nan
Bangaren na Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya shigar da karar ne ta hannun Dr Ahmed Ajuji da wasu mutane 20 inda suka bukaci kotun ta soke kwamitin amintattu na jam’iyyar NNPP da shugabanninta na zartaswa, wadanda suka hada da sakataren kasa, Oginni Olaposi, mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Cif Felix Chukwurah, da kuma lauyanta Tony Obioha.
Sai dai alkalin kotun, mai shari’a M.A. Hassan ya ce kotun ba ta da hurumin sauraren karar, kasancewar lamari ne na cikin gida na jam’iyya.
