DCL Hausa Radio
Kaitsaye

AU ta kori jamhuriyar Nijar daga cikin ta

-

Kungiyar tarayyar Africa ta sanar da korar
jamhuriyar Nijar daga cikin ta, abinda ke zama wani hukunci na baya-bayan nan
da aka yankewa Nijar bayan juyin Mulkin watan jiya.

Bayan taron kungiyar na yau Talata a
birnin Addis Ababa, kungiyar ta ce daukar wannan mataki ya zama wajibi la’akari
da yadda sojojin na Nijar suka ki bada hadin kan da ya dace a game da
tattaunawar Diplomasiyya.

Matakin na AU na zuwa ne bayan da tuni
ECOWAS da wasu kungiyoyin kasashen ketare suka sanar da kakabawa Nijar din
takunkumai, wadanda tuni suka fara tasiri a kanta.

Sai dai kuma masana na ganin
cire Nijar daga cikin AU ba zai yi mata wani tasiri ba, la’akari da yadda kungiyar
ke zama tamkar dai ‘yar amshin shatan kasashen yamma a wasu lokutan.

Bayan wannan
mataki, kungiyar ta AU ta kuma ce zata bibiyi irin matakan da kungiyar ECOWAS
ko CDEAO ta dauka kan jamhuriyar Nijar, don ganin ta inda ya kamata ta kara
shiga da nufin kara matsa lamba ga sojojin na Nijar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ni ne mutum mafi shahara da aka fi caccaka a Nijeriya – Davido

Fitaccen mawakin nan na kudancin Nijeriya David Adeleke wanda aka fi sani da Davido, ya ce shi ne shahararren dan Nijeriya da ya fi fuskantar...

NNPCL bai saka kudin shigar da ya samu na Naira bilyan 500 a lalitar gwamnatin Nijeriya ba a 2024 – Bankin Duniya

Babban Bankin Duniya ya bayyana cewa kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL na biyan kaso 50% kacal na kudaden shiga da aka samu sakamakon cire...

Mafi Shahara