DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kwankwaso ba zai koma jam’iyyar APC ba – Buba Galadima

-

Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi watsi da ikirarin da ake na cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso, na shirin komawa jam’iyyar APC.

Ya ce jam’iyyar NNPP ta bai wa ‘yan Nijeriya damar fahimtar abubuwan da jam’iyyar za ta iya yi ta hanyar ingantaccen shugabanci mai cike da gaskiya da rikon amana.

Google search engine

Idan dai za a iya tunawa a kwanakin baya ne shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr,Abdullahi Umar Ganduje, ya yi hasashen komawar Kwankwaso jam’iyyar APC, inda ya jaddada cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na shirin yin shiga.

Ganduje, wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar magoya bayan Tinubu, wadanda suka kai masa ziyara a Abuja, ya bayyana cewa jam’iyyar APC na ci gaba da karbar fitattun ‘yan siyasa ciki har da ‘yan majalisar tarayya.

Ya kara da cewa jam’iyyar na dakon dawowar Kwankwaso.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan majalisar dokoki 6 a Jihar Zamfara sun fice daga PDP zuwa APC

‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara 6 da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC, suna zargin take...

Kotu ta umurci hukumar EFCC ta gabatar da kwamshinan kudi na jihar Bauchi ga kotu bisa zargin safarar N4.6bn

Kotun Tarayya da ke Abuja ta umurci Hukumar EFCC da ta gabatar da Kwamishinan Kuɗin Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, a ranar 30 ga Disamba domin...

Mafi Shahara