DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Farashin litar man fetur ya tashi daga Naira 860 zuwa Naira 930 a gidajen mai da ke birnin Legas a Nijeriya

-

Google search engine

Gidajen man fetur da ke Legas, a Nijeriya sun kara farashin litar man fetur daga Naira 860 zuwa Naira 930 kan kowace lita, wanda hakan ya sa aka samu karin  akalla naira 70 akan yadda ake siyarwa kwanakin baya.

Tun bayan da kungiyar Human Rights Writers Association of Nigeria HURIWA ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya yi amfani da manyan ofisoshi don ganin an ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar cinikin danyen man fetur tsakanin kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL da matatar mai ta Dangote da sauran matatun mai na ‘yan asalin Nijeriya.

Wasu gidajen mai da ke Legas, irin su MRS Oil & Gas, Ardova da Heyden, tare da yarjejeniya ta musamman da matatar man Dangote, sun daidaita farashin man fetur zuwa sabon farashin.

Sai dai jaridar The Guardian, a ranar Litinin, ta bayyana cewa a baya ana sayar da litar akan naira 860,sai dai zuwa yanzu ya yi tsada da yakai naira 930 a Legas.

Hakazalika, gidajen sayar da man a Legas da makwabciyarta ta jihar Ogun suna sayar da mai a tsakanin Naira 960 zuwa N970 kowace lita.

Sabon tsarin farashin ya biyo bayan sanarwar da Dangote ya bayar na dakatar da sayar da man fetur a naira na wani dan lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

China ta gargadi Amurka game da yi ma Nijeriya barazana da katsalandan

Gwamnatin kasar China ta nuna goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu, tana mai gargadi ga kowace kasa da ke tsoma baki cikin harkokin cikin gidan...

Ba a take hakkin Kiristoci a Nijeriya ba – Babban hafsan tsaron Nijeriya

Babban hafsan tsaron Nijeriya Janar Olufemi Oluyede ya karyata ikirarin cewa ana zaluntar Kiristoci a Nijeriya, inda ya ce babbar matsalar Nijeriya ita ce ta’addanci. Janar...

Mafi Shahara