Tuesday, April 7, 2026
HomeSiyasaJam’iyyar PDP a shirye take domin tunkarar zaben 2027 - Samuel Anyanwu

Jam’iyyar PDP a shirye take domin tunkarar zaben 2027 – Samuel Anyanwu

Sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Samuel Anyanwu, ya bayyana jin dadinsa da irin shirye-shiryen da jam’iyyar ke yi gabanin zabukan 2027 a jihar Imo da Nijeriya.

Anyanwu, ya bayyana hakan ne a karshen mako, lokacin da yake jawabi ga kwamitin zartarwar jam’iyyar PDP a jihar Imo, wanda ya hada da shugabanni da masu ruwa da tsaki a sakatariyar jam’iyyar a Owerri, jihar Imo.

Ya ce dole ne ‘ya’yan jam’iyyar su yi aiki kafada da kafada domin cimma burinsu na kwace mulki hannun APC, yana mai cewa zaben gwamna na da muhimmanci ga jam’iyyar domin karbar mulki a jihar Imo.

Anyanwu ya ce mutanen Imo sun gaji da yaudara da gwamnatin yanzu ke yi don haka akwai bukatar a tsaya kai da fata domin yin nasara a zabuka masu zuwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata